An debawa Kasar Syria wa'adin kwanaki uku

Taron Kungiyar Kasashen larabawa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar Kasashen Larabawa ta debawa kasar Syria kwanaki uku domin ta kawo karshen zubar da jini.

Taron Kungiyar Kasashen Larabawa a Morocco ya debawa gwamnatin Syria wa'adin kwanaki uku domin ta kawo karshen abin da Kungiyar ta kira zubar da jinin al'ummar ta, ta kuma kyale masu sa ido na Kungiyar su tantance halin da ake ciki, ko kuma a kakaba mata takunkumin karya tattalin arziki.

Tun da farko dai, a ranar Laraba magoya bayan gwamnatin kasar ta Syria sun kai hari a kan ofisoshin jakadancin Kasashen Larabawa da dama, ciki har da Kasar Morocco.

Ministan harkokin wajen Kasar ta Morocco, Tayyib Al-Fassi Al-Fihri, ya ce hare-haren ba su da wani alfanu.

Karin bayani