Tarayyar Turai ta tsaurara mataki kan Syria

Shugaban tarayyar Turai Jose Manuel Barroso Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban tarayyar Turai Jose Manuel Barroso

Ministocin tarayyar turai dake taro a Brussels sun amince su kara tsaurara takunkumi a kan Syria.

Sun dakatar da ba ta bashi daga bankin saka-jari na tarayyar turan, sun kuma haramta zirga zirga da bada visa ga wasu karin mutane sha takwas galibinsu jami'an sojan Syriar da ake zargi da hannu a daukar tsauraran matakai kan masu zanga zanga.

Guido Westerwelle, ministan harkokin wajen Jamus, ya ce yana da muhimmanci a ga daukacin wakilan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, sun dauki matsayi guda, su amince da kalaman da zasu yi amfani da su wajen sukar abin da ya kira, rashin imanin da ake gwadawa a Syria.

Karin bayani