Yau ake gudanar da zaben Shugaban Kasa a Gambia

Shugaba Jammeh na Gambia
Image caption Shugaba Jammeh na Gambia

Yau Alhamis al'ummar Kasar Gambia za su kada kuri'a a zaben Shugaban Kasa wanda masu sa ido na Afirka ta Yamma ke cewa za su kauracewa, saboda a cewar su ba za a yi adalci ba.

Shugaba Yahya Jammeh, wanda ya yi juyin mulki shekaru goma sha bakwai da suka gabata, na fatan sake lashe wani wa'adin mulki na shekaru biyar.

Kungiyar ECOWAS ta ce ba za ta aike da masu sa ido ba, saboda linzamin da aka kakabawa kafofin yada labarai da kuma yadda ake muzgunawa 'yan adawa.

Masu fafutukar kare hakkin bil-Adama a Kasar sun ce tuni aka san sakamakon zaben.

Sai dai Shugaban hukumar zabe ta Gambian ya yi watsi da wannan suka, yana cewa ba ta da tushe.

Karin bayani