Sabon farashin mai a Nijar

Taswirar Jumhuriyar Nijar
Image caption Taswirar Jumhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar ma'aikatar ministan man fetur ta bayyana sabon farashin man fetur da zai fara aiki a cikin watan disamba mai zuwa.

A tsarin da ma'aikatar ta yi dai kowane liter daya na mai ko na kanazir zaa sayar da shi sama da dala dari na cfa , yayin da shi kuma butalin iskar gaz mai nauyin kilo 12 zaa sayar da shi sama da jika 3 da rabi na CFA

A yau ne ma'aikatar ministan man fetur din ta bayyana wannan farashin wajen wani taron manema labarai a Yamai .

A karshen wannan watan ne dai gwamnatin kasar ta Nijar za ta yi bikin bude matatar mai ta garin Dan Baki dake yankin Damagaram.

Tuni dai wasu jamaa a kasar ta Nijar su ke ta bude harkokin kasuwanci iri-iri da fatan cin gajiyar arzikin man.

Karin bayani