'Yan adawar Syria sun gaza shawo kan Rasha

zanga zangar adawa da mulkin Assad a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption zanga zangar adawa da mulkin Assad a Syria

Shugaban Babbar jam'iyyar adawa a Syria, Burhan Ghalioun ya ce ya kasa shawo kan Rasha, ta janye adawar ta da takunkumin da kasashen duniya suka kakaba ma Syriar.

Yayinda yake magana bayan shawarwarin da ya yi a birnin Mosko da jami'an kasar ta Rasha, Mr Ghalioun ya tattaunawar ta yi armashi, kodayeke baa samu canjin matysayi daga kowane bangare ba.

A kasar ta Syria kanta kuma, rahotanni sun ce an yi wata mummunar arangama tsakanin dakarun gwamnati da wasu sojoji da suka canza sheka a Arewa maso Gabashin kasar.

Wakilin BBC ya ce masu fafutika na kasar ta Syria sun ce an kashe akalla mutane 70 da suka hada da kananan yara, a cikin kwanaki biyun da suka wuce.

Hakazalika, kafofin yada labaran gwamnatin, sun ruwaito cewa hukumomi sun saki daruruwan fursunoni a matsayin wani bangare na shirin wanzar da zaman lafiyar da Kasashen Larabawa suka gabatar.

Karin bayani