An tarwatsa masu zanga zanga a New York

masu zanga zanga a New York Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption masu zanga zanga a New York

'Yan sanda a New York sun tarwatsa masu zanga-zanga da suka mamaye wani wurin shakatawa dake yankin Wall Street, Hedkwatar kafofin hada-hadar kudi na birnin.

Masu zanga-zangar dai sun tare a wurin ne tun cikin watan Satumban da ya gabata.

Daruruwan 'yan sandan kwantar da tarzoma sun kai samame wurin ne a jiya dad dare don kawar da masu zanga-zangar, inda wasu daga cikinsu suka daure kansu da sarka, suna ta rera wakoki.

'Yan sanda sun kama kusan mutane saba'in. Hukumomin birnin New York sun ce masu zanga-zangar za su iya komawa wurin, amma ba tare da tantunansu ba, da zarar an share wurin.

Wannan kamfe din dai da masu zanga-zangar na New York ke yi, ya sa masu zanga-zanga a sassa daban- daban na duniya sun bi sahunsu.

Karin bayani