Syria; an kai hari ofishin jakadan Maroko

Magoya bayan Shugaba Assad Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Magoya bayan Shugaba Assad

Wasu magoyan gwamnatin Syrian su kai hari akan Ofishin jakadancin Marocco, a Damascus a daidai lokacin da Morrocon ke karbar bakuncin taron kungiyar kasashe Larabawa.

Taron dai ya yi Allah-wadai da yadda Syria ke murkushe masu zanga zangar kin jinin gwamnati.

Shugaban kungiyar, Nabil al-Arabi, ya ce dolene a hada karfi da karfe domin a tsayarda zub da jini a Syria.

Tuni dai Faransa ta janye jakadanta dake kasar saboda rikici.

A yanzu haka dai 'yan adawa a Syria tare da goyon bayan wasu sojoji da su ka sauya sheka sun kai hari akan jami'an tsaron gwamnati, inda su ka kashe guda takwas a yankin Hama. A cikin daren jiya ma sai da suka kai hari a wani sansanin soji dake wajen garin Damascus.

Karin bayani