Mario Monti zai aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sabon Fira Ministan, Italiya, Mario Monti

Sabon Fira ministan Italiya, Mario Monti ya gabatar da shirinsa na magance matsalar tattalin arziki da kuma rage bashin da ake bin kasar.

A jawabinsa na farko ga majalisar dokokin kasar ya ce za'a aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu da habaka tattalin arzki da kuma adalci a rayuwar yau da kullum kafa da kafada.

Ya ce; "Makomar euro ya dogara akan irin matakan da Italiya za ta dauka a makwanni masu zuwa, ba wai gaba daya akan italiya ba, amma wani bangare.

"Masu zuba jari na kasashen waje su ne ke bin kusan rabin bashin da ake bin kasarnan.

"Dole mu gamsar da su cewa mun dau hanyar tabbatar da rage bashin da ake binmu da kuma habakar kasar a cikin gida." In ji Mario Monti

Haka kuma yayi alkawarin yaki da kin biyan haraji, kuma shirinsa ba zai fidda batun daukar manyan matakai akan gungun masu zullewa biyan harajin ba.

"Ba za mu fidda batun daukar kwararan matakai kan gungun masu aikata laifuka da dukkan masu kaucewa biyan haraji ba a shirin sake habaka tattalin arzikin kasarmu."

Sai da yayinda sabon Firai ministan ke wannan jawabin dubban dalibai masu zanga-zanga ne suka nufi majalisar dattawan a birnin na Roma.

Zanga-zangar ta kin amincewa da rage kasafin kudi da karuwar rashin aikinyi ta zo daidai da yajin aikin ma'aikatan sufuri a fadin kasar.

Karin bayani