Shugaba Ouattara ya kammala ziyara a Nijar

Shugaba Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Shugaba Alassane Ouattara

A jamhuriyar Nijar da yammacin nan ne shugaba Alasan Ouattara na Cote-d'Ivoire, ya kammala wata ziyarar aikin da ya kai a kasar don karfafa dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaban na Cote d'Ivoire da shugaba Alhaji Isoufu Mahamadou na Nijar, sun tattauna a kan yadda za su inganta hanyoyin habbaka tattalin arzikin kasashen nasu da ma kyautata dangantaka tsakanin kasashen Afrika ta yamma, wakilan kungiyar Conseil de l'Entente.

Wani muhimmin batu da shugabannin biyu suka tabo, shi ne na shimfida layin dogo tsakanin kasashen biyu da kuma tagwayen hanyoyi da za su tashi daga Abidjan zuwa Ouagadougou na Burkina Faso, sannan su karaso birnin Yamai na Jumhuriyar ta Nijar.

Shugaba, Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire, har ila yau ya dauki alkawarin fadakar da 'yan kasuwar kasarsa da su je su saka jari a kasar ta Nijar.

Karin bayani