Alasanne Outtara na ziyara a Nijar

Shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Outtara Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Outtara

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alasan Watara na yin wata ziyarar aiki ta yini daya a jamhuriyar Nijar, inda zai tattauna da shugaba Alhaji Isufu Mahamadu da sauran mahukuntan kasar.

Duk da cewa dai ba a san abin da za su yi magana takamaimai a kai ba, ana jin cewa za su tabo huldar da ke tsakanin kasashen biyu ne, wadanda dukansu mambobin kungiyoyi da dama ne na yankin Afrika ta yamma.

Kasashen na Nijar da Cote d'ivoire dai nada hulda daddiya a tsakaninsu.