Majalisar wakilai za ta yi muhawara game matakan gwamnatin Italiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Majalisar dokokin Italiya

A ranar Juma'a ne ake sa ran majalisar wakilan Italiya za ta kada kuri'ar karshe kan matakan shawo kan tattalin arzikin da sabuwar gwamnatin kasar ta bullo da su.

A ranar Alhamis, majalisar dattawa ta amince da shirin da gwamnatin Mario Monti ta fito da su, wadanda ake ganin za su magance matsalar tabarbarewar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Babban kalubalen da ke gaban gwamnatin dai shi ne na rage dimbin bashin da ke kan kasar.

A jawabinsa na farko ga majalisar , Mr Monti ya ce, za a daidaita matakan tsuke bakin aljihun gwamnati ne ta hanyar ci gaban tattalin arziki da kuma adalci a zamantakewar al'uma.

Ya ce makomar kudin Euro za ta dogara ne a kan matakan da Italiya za ta dauka a cikin 'yan makwanni masu zuwa.

Jam'iyyu na goyon bayansa

Zuwa yanzu dai, kusan daukacin jam'iyyun kasar sun bayyana cewa za su goyi bayan gwamnatin Mr Monti.

Sai dai har yanzu, tsohon Firayim ministan, Silvio Berlusconi, na da goyon baya sosai a majalisar dokokin kasar, kuma ya ce ba zai yi wata-wata ba, wajen durkusar da gwamnatin Mr Monti, idan har ya gano cewa ba ta daukar matakan da yake ganin sune za su ceto tattalin arzikin kasar.

Mr Monti, da jami'an gwamnatinsa, wadanda kwararru ne a harkokin kudi sun karbi ragamar tafiyar da kasar ce, a yayin da take fuskantar matsanancin tabarbarewar tattalin arziki.

Karin bayani