Jama'a na kokawa da farashin mai a Nijar

A jamhuiyar Nijar yau ne ministan makamashi da man fetur, Malam Foumakoye Gado ya bayyana gaban yan majalisar dokokin kasar domin yi mu su bayani a kan farashin man kasar ta Nijar , wanda yan kasar za su fara amfani da shi a watan disamba mai zuwa idan Allah ya yarda.

Ministan dai ya yi kokarin kare hujjojinsa na kai farashin man a dala kusan dari da 20 na sefa duk da cewa man da kasar ke shigowa da shi daga kasashen waje bai kai dala dari da 40 ba na sefa.

Galibin yan kasar ta Nijar da suka hada da 'yan majalisan dai ba su goyi bayan gwamnatin ba kuma sun yi kira da ta sake duba farashin ta yadda zai zo wa talaka da rangwame.