Aung San Suu Kyi za ta shiga zaben da za a yi a Burma

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Aung San Suu Kyi

Jam'iyyar da mai fafutukar tabbatar da mulkin dimokaradiyyar Burma, Aung San Suu Kyi, ke jagoranta ta ce za ta shiga zaben da za a gudanar a kasar nan ba da dadewa ba.

Jam'iyyar ta ce za ta shiga zaben ne bayan da ta gamsu da sauye-sauyen da gwamnatin kasar ke gudanar wa a harkokin siyasar kasar.

Hakan na zuwa ne a yayin da shugaban Amurka Barack Obama zai tura sakatariyar harkokin wajen kasar, Hillary Clinton, zuwa Burma a watan gobe - a wata ziyara irinta ta farko cikin shekaru hamsin.

Ziyarar na da nufin duba hanyoyin da Amurka za ta taimaka wajen kawo sauye-sauyen siyasa da kuma sasantawa a kasar.

Shugaba Obama ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a kasar Indonesia.

Mr Obama ya ce ya dauki matakin ne bayan tattaunawa kai-tsaye a karon farko da jagorar 'yan adawar kasar, Aung San Suu Kyi.

Ya ce ana samun kwarya-kwaryar ci gaba daga mahukuntan Burma, amma ya ce akwai bukatar kari.

Karin bayani