Matsalar rashin tsabtataccan ruwan sha

Matsalar ruwan sha a Afirka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Matsalar ruwan sha a Afirka

Wani rahoto da kungiyar tabbatar da samun tsabtataccen ruwan sha ta duniya ta fitar a yau ya yi gargadin cewa gwamnatoci da dama a nahiyar Afirka basa wani abin azo a gani wajen samar da tsabtataccan ruwan sha da muhalli, abinda ke jefa rayukan miliyoyin mutane cikin hadari.

Dama dai daya daga cikin tanade tanaden shirin muradun karni shi ne rage rabin yawan mutanen da suke da matsalar tsaftar muhallin , su miliyan dubu 2 da miliyan 500 zuwa shekara ta 2015.

Sai dai kuma rahotan ya ce za'a dauki shekaru dari biyu a Afirka kafin akai ga cimma matsayin da aka sa dangane da samar da tsabtataccan ruwansha da muhalli a cikin muradin karni.

Matsalar rashin tsaftar dai ita ce ke haddasa cutar amai da gudawa, cutar da tafi hallaka yara a nahiyar Afrika da kuma kudancin Asia.

Karin bayani