Shugaban Amurka ya gana da na China

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wen Jiabao tare da Obama

Shugaba Barack Obama na Amurka ya tattauna da Firayim Ministan China, Wen Jiabao, a wajen taron kasashen Kudu maso Gabashin Asia da ake gudanar wa a Indonesia.

Babu dai wata sanarwa a hukumance kan abubuwan da suka tattauna akai, sai dai ganawar ta zo ne a lokacin da ake samun bambance-bambance tsakanin kasashen biyu.

Kasashen dai na da bambancin ra'ayi kan 'yancin yankin Kudancin kogin China, wanda China ke kallo a matsayin yankinta, kuma ta yi gargadi kan duk wani katsalandan daga kasashen waje.

Kazalika kasashen biyu na sa-in-sa kan batun darajar kudin China, inda Amurka ke cewa Chinan na rage darajar kudinta domin ta samu riba a harkar kasuwanci, matakin da Amurkan ke Alla-wadai da shi.

Karin bayani