Assad ya ce Syria za ta ci gaba da murkushe 'yan adawa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Syria, Bashir Assad

Shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad, ya ce kasarsa ba za ta bayar da kai bori ya hau ba, ga matsin lambar da kasashen duniya ke yi mata, kuma za ta ci gaba da murkushe 'yan bindigar da ya ke zargi da haddasa fitina a kasar.

A wata tattauna da ya yi da jaridar Sunday Times, Mr Assad ya ce 'yan bindiga ne ke da alhakin duk rikice-rikicen da kasar ke fama da su.

Ya ce: ''Idan ana magana game da kashe-kashe, ya kamata a tambaya cewa, su waye suka kashe sojoji, da 'yan sanda dari takwas akan titunan Syria.? Don haka yanzu ba wai ana batun zanga-zangar zaman lafiya ba ne, a'a ana maganar 'yan bindiga ne.Kuma duk lokacin da aka ce akwai 'yan bindiga a waje, to dole a samu kashe-kashe''.

Mr Assad ya ce hukumomi za su gudanar da bincike game da zargin musgunawa jama'a da ake yi wa jami'an tsaron kasar, yana mai cewa zai tabbatar da adalci a binciken.

An kai hari kan ofishin jam'iyyar Assad

A birnin Damascus kuwa, wani hari aka kai da rokoki da gurneti kan ofishin jam'iyyar Baath ta shugaba Assad.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce an ga hayaki yana tashi a ginin.

Sai dai wani wakilin sashin Larabci na BBC da ke wurin da lamarin ya faru, ya ce babu wata illa da harin ya haifar, amma ya ce mazauna yankin sun ce an dade ana musayar harbe-harbe.

Wannan ne dai karo na farko da masu adawa da gwamnatin ta Syria suka kai hari a birnin na Damascus.

Wa'adin kasashen Larabawa

Wadannan kalamai na Mr Asad na zuwa ne daidai cikar wa'adin da kungiyar Larabawa ta baiwa kasar don ta amince da shigar masu sa ido na kungiyar cikinta, ko kuma ta fuskanci takunkumin karya tattalin arziki.

Shugaba Assad dai ya zargi kungiyar kasashen Larabawan da kasancewa 'yar kan-zagin kasashen Yamma wajen katsalandan a harkokin Syriar.

Ya kara da cewa duk wani hari kan kasar, zai haifar da wata girgizar kasa da za ta dagula yankin Gabas ta Tsakiya.

Karin bayani