Za a yi wa Saif al-Islam shari'a a Libya, in ji gwamnati

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saif al-Islam a lokacin da yake cikin jirgi

Hukumomin gwamnatin rikon kwarya a Libya sun ce za a yi wa Saiful Islam, dan marigayi shugaba Kanal Gaddafi, shari'a mai adalci.

Ministan shari'a na kasar, Mohammed al-Alagi, ya ce za a gudanar da shari'ar Saif al-Islam a Libya.

Mr Agali ya ce yawancin laifukan da ake zargin Saif al-islam da aikata wa, ya aikata su ne a kasar, don haka kasar ce ta cancanci hukunta shi.

Ya ce ya tabbatar wa da babban mai shigar da kara na kotun masu aikata manyan laifuka ta duniya, Luis Moreno Ocampo, cewa za a yiwa Saif al- islam din adalci.

'Yan kasar dai na ci gaba da murna tun bayan da aka sanar da kama Saif al-islam.

An kama shi ne a yankin kudu maso yammacin kasar a yayin da yake kokarin ketarawa zuwa jamhuriyar Nijar.

Karin bayani