Masu zanga-zanga na fafata wa da 'yan sanda a Masar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban masu zanga-zanga a Masar

'Yan sanda da masu zanga-zanga a kasar Masar na ci gaba da kai-ruwa-rana, bayan 'yan sandan sun hana masu zanga-zangar kaiwa ga dandalin Tahrir da ke Alkahira, babban birnin kasar.

Masu zanga-zangar na so ne mahukuntan sojin kasar su mika mulki ga gwamantin farar hula.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar na jifa kan shingayen da 'yan sandan kwantar da tarzoma suka kafa a hanyoyi biyu da ke kaiwa ga dandalin Tahrir.

Tun da farko dai, 'yan sanda sun yi amfani da harsasan roba da barkonan tsohuwa kan masu zanga-zangar, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata fiye da dari shida.

Tarzomar dai na zuwa ne 'yan kwanaki kadan kafin zaben 'yan majalisar dokoki na farko, tun bayan kifar da gwamnatin Hosni Mubarak.

Karin bayani