An kama Saif al-Islam Gaddafi

Saif al-Islam Gaddafi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saif al-Islam Gaddafi

Gwamnatin wucin gadin Libiya ta bada sanarwar kama Saif al-Islam Gaddafi, dan tsohon shugaban kasar.

An ce wasu mayaka ne dake yankin Zintan a kudu maso yammacin Libiyar suka kama shi, tare da wasu mukarrabansa.

An rika jin karar harbe harben bindigogi na murna a cikin babban birnin Libiyar, bayan rahotannin cewa an kama Saif al-Islam Gaddafin.

Wani kwamandan dakarun Libyar ya ce an kama Saif al Islam ne a garin Obari mai dausayi dake cikin hamada a kudancin Libyar.

An ce yana kan hanyarsa ce ta shiga jamhuriyar Nijar, inda dan uwansa Saadi ya nemi mafaka. Yanzu haka dai an ce an kai Saif al-Islam garin Zintan wanda ke kudu maso yammacin Tripoli. An kuma ce yana cikin koshin lafiya.

Kotun shari'ar miyagun laifufuka ta duniya dai na neman Saif al-Islam ruwa a jallo, bisa zargin aikata laifufukan yaki da cin zarafin bil'adama.

Gidan talabijin din Libiyar ya nuno hotunan wani mutum mai kama da Saif al-Islam din. An dai ce kowane lokaci daga yanzu za a kai Saif al-Islam din birnin Tripoli.

Babban mai gabatar da kara a kotun duniya mai shari'ar mugayen laifufuka, Luis Moreno Ocampo, ya ce zai je Libiya a mako mai zuwa, domin tattaunawa da hukumomin wucin gadin kasar, a kan wurin da ya kamata a yi masa shari'a.

Karin bayani