Matsalar 'yan kalare ta dawo Gombe

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga jihar Gombe da ke arewacin Nijeriya na cewa matsalar nan ta matasa 'yan daba da ake kira 'yan kalare wadanda kan aikata ta'asa da makamai ta sake kunno kai, bayan ta lafa na wani lokaci.

Jama'a sun ce 'yan dabar na kashe mutanen da basu ji ba- basu-gani ba, abin da ya sanya ake nuna damuwa. 'Yan adawa a jihar dai na zargin gwamnati da yin sakaci wajen yaki da matsalar ta kalare da kuma ba 'yan kalaren kudi, lamarin da suka ce shi ya sanya suka sake bayyana.

Sai dai gwamatin na musanta zargin tana mai cewa tana daukar matakan baiwa matasa aikin yi. Jihar ta Gombe dai ta kwashe shekaru da dama tana fama da wannan matsala, inda ake zargin 'yan siyasa da amfani da matasan domin cimma burinsu na siyasa.

Karin bayani