Ana ci gaba da tashin hankali a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga a Syria

A ranar Juma'a an ci gaba da fuskantar tashin hankali a kasar Syria, a daidai lokacin da wa'adin da kungiyar Larabawa ta debarwa gwamnatin kasar na kawo karshen murkushe masu zanga-zanga ke cika.

Rahotanni na baya-bayan nan sun ce jami'an tsaro sun kashe mutane goma sha daya.

Amurka da Turkiyya sun yi gargadin cewa rikicin na iya rikidewa zuwa yakin basasa.

Sai dai Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce ba ta hasashen tsoma hannun kasashen duniya a rikicin kasar, kamar yadda ya faru a Libya.

Tun da farko rahotanni sun ce Syria ta amince kungiyar kasashen larabawa ta aika da karamar tawaga, ba mutum dari biyar da kungiyar ta ce ba, domin sanya ido kan abin da ke faruwa a kasar.

Karin bayani