Paparoma ya kare ziyara a jamhuriyar Benin

Paparoma Benedict a Jamhuriyar Benin Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Paparoma Benedict a Jamhuriyar Benin

Paparoma Benedict ya kammala ziyarar da ya kai kasar Benin.

A yau ya shugabanci addu'o'i a filin Allah Ta'ala a birnin Cotonou, wadanda dubban jama'a suka halarta.

Daga cikin mahalartan har da shugabannin cocin Roman Katolika masu mukamin Bishop, su fiye da dari biyu, daga dukan nahiyar Afirka.

Wakilin BBC a fadar Vatican ya ce, a lokacin ziyarar Paparoman a kasar ta Benin, ya tabo batutuwa da dama masu sarkakiya.

Daga cikinsu akwai batun tuntubar juna tsakanin mabiya addinin Krista da Musulmi, da batun annobar cutar Aids ko SIDA, sannan da yadda za a samu daidaito tsakanin koyarwar da cocin Roman katolika ke yi da kuma addinan gargajiya na Afirka.

Karin bayani