An kama Abdullah al-Sanusi a Libiya

Mayaka a Libiya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mayaka a Libiya

Gwamnatin wucin-gadin Libiya ta ce, an kama tsohon babban jami'in leken asirin kasar, Abdullah al-Sanusi, a yankin kudancin kasar.

Abdullah al Sanusi yana da dangantaka ta fuska biyu da marigayi Kanar Gaddafi: watau a matsayin babban jami'in leken asirinsa, da kuma surukinsa.

Tun shekaru da dama da suka wuce ne ake danganta shi da irin ta'asar da gwamnatin Gaddafi ke yi.

'Yan Libiya sun dorawa Abdullah Al Sanusin alhakin mummunan kisan kiyashin 1996, lokacin da aka hallaka fursunoni fiye da dubu guda, a gidan kurkukun Abu Salim da ke birnin Tripoli.

An kuma ce, tsohon jami'in leken asirin, wanda a yanzu shekarun sa sittin da biyu a duniya, ya taka muhimmiyar rawa a yunkurin murkushe boren da aka fara a birnin Benghazi, a watan Fabrairun da ya wuce.

An ce shi ke da alhakin kashe-kashen da aka yi a Benghazin, da kuma daukar sojan haya daga kasashen waje.

Abdullah al Sanusi shine dan Libiya na karshe da kotun duniya mai shari'ar muggan laifufuka ke nema, bayan Saif al-islam, dan kanar Gaddafi, ya shiga hannu a ranar asabar.

Karin bayani