Kungiyar Larabawa tayi watsi da shawarwarin Syria

Magoya bayan shugaba Bashar al-Assad Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Magoya bayan shugaba Bashar al-Assad

Kungiyar kasashen Larabawa ta yi watsi da sauye-sauyen da Syria tayi wa wani shirin da ta gabatar, na neman kawo karshen tashin hankalin da ake yi a kasar.

Majalisar dinkin duniya ta ce, tun daga watan Maris kimanin mutane dubu ukku da rabi ne suka hallaka, a tashe tashen hankula a Syriar.

A cewar kungiyar Larabawan, gyaran da kasar Syriar ta yi wa shawarar da ta gabatar, zai sauya fasalin aikin tawagar da kungiyar ke son turawa zuwa Syriar.

A cikin wata hira da jaridar Sunday Times ta nan Birtaniya, shugaba Assad na Syriar ya ce, kungiyar kasashen Larabawar na share fage ne domin kasashen waje su kaiwa kasar hari.

Karin bayani