An kama mutumin da ake zargi da ta'addanci a Amurka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Obama

Mahukunta a Amurka sun kama wani mutum mai suna, Jose Pimente, da ake zargi da yunkurin dana bam a wurare daban-daban na birnin New York.

Magajin garin New York, Michael Bloomberg, ya ce Mr Pimentel ya shirya kai hari a kan motocin 'yan sanda da sojojin da ke dawo wa daga Afghanistan da kuma Iraqi.

Ya ce Mr Pimentel na goyon bayan kungiyar al-Qaeda.

'Yan sanda sun ce sun yi ta sanya ido a kan Jose Pimentel ne tun daga watan Mayun shekarar 2009.

Sun ce ya koyi yadda ake hada bama-baman da ake yi a gida ne, bayan da ya karanta wata mujalla da kungiyar Al-Qaeda ke wallafa a shafinta na internet.

Daga nan, a cewar 'yan sandan, ya fara sayen kayayyakin da ake hada bama-bamai da su, wadanda suka hada da bututu, da kusoshi, kuma ya yi hakan ne cikin lura.

Ba dan kungiyar 'yan ta'adda ba ne

An dai kama Mr Pimental ne a lokacin da yake hada wani bam a gidansa da ke Manhattan, kuma magajin garin birnin New York, Mike Bloomberg, ya ce Mr Pimental shi kadai ne ke harkokinsa, ba tare da tsoma bakin kungiyoyin 'yan ta'adda na kasashen waje ba:

''Mutumin da ake zargin shi kadai ne ke harkokinsa, saboda kawai nuna kiyayyarsa game da kasancewar dakarun Amurka a kasashen Iraq da Afghanistan, kuma da alama yana koyi ne da kungiyar al-Qaeda. Amma baya cikin gaggan kungiyoyin 'yan ta'adda na kasashen waje.

Hukumomi dai sun bukaci a tsare Mr Pimental a gidan yari har sai an kammala binciken da ake yi akan sa.