Mutane dayawa sun hallaka a zanga zanga a Masar

Zanga zanga a Masar Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zanga zanga a Masar

Ma'aikatar lafiya ta kasar Masar ta tabbatar da mutuwar mutane fiye da talatin, da kuma raunata wasu kusan dubu daya da dari takwas, a kwanaki biyun da aka kwashe ana dauki-ba-dadi tsakanin masu zanga zanga da jami'an tsaro a Alkahira, babban birnin kasar.

Sojoji da 'yan sanda sun rika harbi da harsasai na roba, a kokarin tarwatsa masu zanga zangar da suka yi dafifi a dandalin Tahrir, dandalin da a can ne aka shirya gangamin da yayi sanadiyar kifar da gwamnatin shugaba Mubarak a watannin baya. Masu zanga zangar na korafin cewar, sojoji na kara yin babakere kan harkokin mulki, suna bukatar jagoran sojan da ya sauka.

Jam'iyyun siyasa 25 a kasar ta Masar sun yi kira da a kori ministoci biyu: wato na yada labarai da na harkokin cikin gida, akan tashin hankalin da ake fama dashi a kasar.

Cikin jam'yyun da suka yi wannan kira har da jam'iyyar 'yan uwa Musulmi.

Tun farko dai ministan raya al'adun kasar ya ajiye aikinsa, don nuna bacin ransa akan yadda jami'an tsaro ke tinkarar zanga zangar.

Karin bayani