'Yan majalisar Najeriya ba su gamsu da kasafin kudi ba

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Taswirar Najeriya

'Yan majalisar wakilan Najeriya sun ce ba su gamsu da yadda bangaren zartarwa ya aiwatar da kasafin kudin kasar na bana ba.

Sun ce bangaren zartarwar bai gudanar da ayyukan da ya shaida wa majalisar zai yi a lokacin da ya mika mata kasafin kudin don amincewar ta ba.

Alhaji Musa Sarki Adar wani dan majalisa ne, ya shaida wa BBC cewa ma'aikatan gwamnati ne ke da alhakin rashin aiwatar da kasafin kudin sakamakon watsin da suka yi da ayyukan, a lokacin da 'yan siyasa suka tafi yakin neman zabe.

Sai dai ya ce majalisar za ta tabbatar an aiwatar da kasafin kudin badi, wanda za a gabatar mata nan ba da dadewa ba.

A Najeriyar dai, an sha samun takaddama tsakanin 'yan majalisa da bangaren zartarwa game da aiwatar da kasafin kudi.

Karin bayani