Cutar shan inna na karuwa a Najeriya

Rigakafin cutar shan inna Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rigakafin cutar shan inna

Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta Najeriya ta ce alkalumma na baya-bayanan sun nuna cewar, yawan wadanda suka kamu da cutar shan inna a kasar, a wannan shekarar, ya tashi zuwa 43 a cikin makonnin baya-bayanan.

A watan Satumba, ministan lafiya na kasar ya tabbatar da cewar, mutane 29 ne aka gano sun kamu da cutar a jihohi shidda, daga farkon wannan shekarar.

A lokacin taron kasashen Commonwealth da aka yi a watan da ya wuce a Australia, shugaban Najeriyar, Goodluck Jonathan, ya yi alkawarin kara yawan kudaden da kasar ke warewa don yaki da cutar ta Polio, daga dala miliyan 17 zuwa miliyan 30 a shekara mai zuwa.

Shugaban hukumar ta kula da kiwon lafiya a matakin farko ta Najeriyar, Dr. Ado Jeji Muhammad, ya shaidawa BBC cewa, sun sha alwashin ganin bayan cutar ta shan inna, duk kwa da koma bayan da ake fuskanta.

Karin bayani