Cutar AIDS ta ragu sosai a duniya

Kwayar cutar HIV Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Kwayar cutar HIV

Hukumar yaki da cutar AIDS ko SIDA ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, an samu raguwa mafi girma ta kamuwa da kwayar cutar HIV, tun bayan da aka samu barkewar annobar cutar mafi girma shekaru sha hudu da suka wuce.

A wani sabon rahoto, hukumar ta UN-AIDS ta ce, matakan da ake dauka a kasashen duniya, na tunkarar cutar, sun tilasta raguwar yaduwarta da sama da kashi 20 cikin 100.

Adadin masu mutuwa a sakamakon cutar shi ma ya ragu, sanadiyyar shan magunguna.

Sai dai an yi gargadin cewa, a wasu kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara, har yanzu cutar na ci gaba da yaduwa .

Karin bayani