Zaa matso da zaben shugaban kasar Masar kusa

Field Marshall Hussein Tantawi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Field Marshall Hussein Tantawi

Shugaban Majalisar koli ta sojojin Masar ya amince da murabus din majalisar ministocin kasar.

Field Marshall Hussain Tantawi wanda ya yi wa ya jama'ar kasar jawabi kai tsaye ta gidan Telbijin din kasar, ya kuma ce za'a matso da zaben shugaban kasar kusa.

Ya ce ya yi alkawarin gudanar da zaben 'yan majalisa a lokacin da a tsara, kuma za'a gudanar da zaben shugaban kasa kafin karshen watan Yulin badi.

Field Marshall Hussein Tantawi ya kara da cewa sojoji ba su da burin karbe mulki a Masar.

Fiye da mutane 20 ne dai suka mutu a zanga -zangar da ake yi a kasar ta Masar tun daga ranar Asabar din da ta gabata.

Karin bayani