Gubar dalma ta hallaka karin yara a Najeriya

Wasu masu hakar ma'adinai a Zamfara Hakkin mallakar hoto b
Image caption Wasu masu hakar ma'adinai a Zamfara

Hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya ta tabbatar da mutuwar yara akalla 11 sakamakon sabuwar bullar cutuka masu alaka da shakar gubar dalma da ke fitowa daga wuraren hakar zinare a kasar.

Shugaban hukumar ta Center For Disease Control, NCDC, ya shaidawa BBC cewar yaran da suka mutum na daga cikin sabbin mutane 22 da aka gano sun kamu da cutar da gubar dalmar ke haddasawa a cikin wannan watan a jahohi ukku na kasar.

Sai dai ya ce, mafi yawansu, suna jahar Zamfara ne, inda cutar ta hallaka fiye da mutane 400 a bara.

A makon jiya Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewar za'a iya kawar da matsalar kawai inda aka sauya yadda ake hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a jahar.

Karin bayani