An gurfanar da Ali Ndume a Kotu bisa zargin alaka da Boko Haram

Harin Boko Haram a Damaturu Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumar leken asiri ta Najeriya SSS ta gurfanar da Sanata Ali Ndume, dan majalissar dattawa daga jihar Borno a gaban kuliya bisa zargin alaka da kungiyar Jama'atu Ahlussunna lid-da'awati wal jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram.

Hukumar ta gurfanar da shi ne tare wani da yake ikirarin yana magana ne da yawun kungiyar Boko Haram mai suna Ali Sanda Umar Konduga wanda aka fi sani da Usman Al-zawahiri a kafofin yada labarai.

An dai kama Senator Ali Ndume ne a jiya, bisa zargin yana da hannu wajen daukar dawainiyar kungiyar Boko Haram zargin da ya musanta a gaban kotu.

Sai dai a baya kungiyar ta Boko haram ta nesanta kanta da shi Al-zawahirin inda ta ce ba ya magana da yawunta , kuma ma ta yi zargin jami'an tsaro ne suka dasa shi domin ya rika ikirarin magana a madadinsu.

Hukumar ta SSS ta ce tun a ranar uku ga watan Nuwamban da ya gabata ne wasu jami'an tsaro na hadin gwuiwa suka kama Ali Sanda Umar Konduga wanda aka fi sani da Usman Alzawahir a kafofin yada labarai a unguwar Gwange dake Maiduguri.

Sanarwar da mai magana da yawun hukumar ta SSS Merylin Ogar ta sanya wa hannu ta ce, kame Al-zawahir ya kara tabbatar da matsayin hukumar cewa wasu 'yan siyasa ne ke daukar nauyin aikace-aikacen kungiyar ta Boko Haram.

Sanarwar ta hukumar SSS ta ce Konduga tsohon dan daban siyasa ne na wata kungiya da aka fi sani da ECOMOG, wanda wani dan siyasa a Maidugurin jihar Borno ya dauke shi aiki kuma ya yi alkawarin biyansa naira miliyan goma, sai dai dan siyasan ya rasu a lokacin da yake kan hanyar sa ta kawo masa naira miliyan biyar a matsayin kafin alkalami.

Hukumar ta SSS ta kuma ce a bayanan da ta tatsa a wajen Al-zawahiri, ya shaida mata cewa, bayan rasuwar wancan da siyasar, sai Sanata Ali Ndume daga jihar ta Borno ya ci gaba da gudanar da al'amuransa, inda ya umarce shi da ya aike da sakwannin barazana ta wayar salula ga manyan mutane da dama a kasar ciki har da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, da gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, da gwamnan Naija Babangida Aliyu da kuma shugaban kotun sauraron kararrakin zabe dake da mazauninta a Maiduguri, don ta tabbatar ta soke zaben gwamnatin dake ci a jihar abinda ya sa aka suya wa kotun zaben mazauni zuwa Abuja.

Hukumar ta SSS ta kuma ce binciken da suka yi a wayar Al-Zawahir ya nuna cewa akwai tuntubar juna akai-akai tsakanin sa da Sanata Ali Ndume.

A baya dai kungiyar jama'atu Ahlussuna Lidda'awati wal jihad wadda aka fi sani da Boko Haram, ta nesanta kanta da Al-zawahiri inda ta ce a yanzu tana zargin jami'an tsaro ne suka dasa shi domin ya bata musu suna.