Majalisar tsarin mulkin Tunisia ta zauna

Wurin zaman majalisar Tunisia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wurin zaman majalisar Tunisia

A yau ne majalisar da aka zaba a Tunisia don rubuta wa kasar sabon kundin tsarin mulki, ta yi zaman ta na farko.

A watan jiya ne aka zabi 'yan majalisar, kuma wata jam'iyya mai kishin Islama, da a baya aka haramtawa shiga harkokin siyasa ce ta samu wakilci mafi girma a majalisar.

An dorawa majalisar alhakin rubutawa kasar sabon kundin tsarin mulki da zai share fagen gudanar da zabuka a kasar.

Wani boren jama'a da aka yi a watan Janairu, ya yi sanadiyar raba shugaba Zain Albidin Ben Ali da mulkin kasar.

Daga nan ne kuma aka samu watsuwar boren jama'a a wasu kasashen Larabawa.

Karin bayani