An ganawa mutane azaba a Bahrain

Bahrain Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugaban wani kwamiti mai zaman kansa da ya binciki yadda aka yi amfani da karfi wajen murkushe zanga zangar neman tsarin demokradiya a Bahrain, ya bada bayanan yadda a ka ci zarafin dadama daga cikin wadanda aka tsare.

Cherif Bassouini yace an rufe fuskokin mutanen, kana aka yi masu bulala, sannnan aka dodana musu wayar lantarki harma da barazanar fyade don kawai a tatsi bayanai daga wurinsu.

Rahoton wanda kwamiti mai zaman kansa ne ya shirya shi, yayi matukar sukar gwamnatin kasar, wacce tuni ta amince cewa dakarunta sun yi amfani da karfi fiye da kima.

Haka kuma akwai rahotannin dake cewa gwamnati na muzgunawa likitocin da suka kula da wadanda suka samu raunuka a cikin masu zanga-zangar.

Dr. Fatima Hajj, na daga cikin likitocin da suka kula da wasu daga cikin masu zanga-zangar a babban asibitin Bahrain. Ta kuma ce an dakatar da ita daga aiki yayinda aka yanke mata hukuncin daurin shekaru biyar bisa zargin hada baki a ture gwamnatin ta Bahrain.

Shugaban kwamitin ya ce gwamnatin kasar ta Bahrain ba ta dauki mataki a kan wadanda ke da hannu a wannan al'ammari ba, kuma hakan ya sabawa dokokin kasar.

Shugaban Hukumar mai zaman kanta, ya ce wannan shi ne karon farko da wata kasa a yankin ta gudanar da bincike bisa radin kanta a kan tashin hankalin da ya faru a cikin kasar, ba tare da matsin lamba daga kasashen waje ba.

Karin bayani