Jonathan ya sauke Farida Waziri daga shugabancin EFCC

Farida Waziri Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Tsohuwar shugabar EFCC, Farida Waziri

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sanar da sauke shugabar hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC Madam Farida Waziri daga mukaminta.

Shugaban ya kuma sanar da umarnin nada Mallam Ibrahim Lamurde a matsayin shugaban hukumar EFCC na riko.

Sanarwar da ta fito daga fadar shugaban kasa dauke da sa hannun mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yada labarai Dr Reuben Abati ba ta yi karin bayani kan dalilin sauke Farida Wazirin daga mukaminta ba.

Kokarin samun karin bayani daga mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin yada labari Reuben Abati ya ci tura, kuma jami'ai a ofishinsa sun ce babu wani karin bayani da aka yi musu kan dalilan cire ta.

Zargin cin hanci

Can ma a hukumar ta EFCC, wasu jami'an da muka tuntuba sun ce su ma a kafofin yada labarai suka samu labarin, domin i zuwa maraicen ranar Talata, tsohuwar shugabar ta EFCC Farida Waziri ta jagoranci wani zama da ya tattauna kan shirye-shiryen ranar yaki da cin hanci da rashawa da ake shirin gudanarwa nan gaba.

Tsohuwar shugabar hukumar ta EFCC Madam Farida Waziri ta sha suka daga bangarori da dama da ke zarginta da sako-sako kan yadda take tunkarar yaki da cin hanci da rashawa a kasar, sabanin wanda ya gabace ta Mallam Nuhu Ribadu.

A baya ma wasu kafofin yada labarai sun wallafa wasu zarge-zargen aikata cin hanci da rashawa a kanta amma ta musanta, inda ta ce a karkashin ikonta ta zafafa yaki da cin hanci da almundahana a kasar.

Sabon shugaban riko na hukumar ta EFCC Mallam Ibrahim Lamurde dai jami'in hukumar 'yan sandan Najeriya ne, kuma kafin nadin nasa shi ne daraktan gudanarwa na hukumar ta EFCC. A baya dai ya taba rike mukamin shugabancin hukumar na riko kafin tsohon shugaban Najeriya marigayi Umaru Musa 'Yar'adua ya nada Farida Waziri a matsayin shugabar hukumar ta EFCC a shekarar 2008.

Yaki da cin hanci ya yi rauni a Najeriya

A watan Agustan da ya gabata ne kungiyar Human Rights Watch mai kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa, ta ce yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya na fuskantar zagon kasa daga bangarori da dama a Najeriya.

A wani rahoto da kungiyar ta fitar a kan hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, ta ce hukumar da Majalisun kasar da ma fadar gwamnati sun taimaka wajen dakile aikin yaki da dabi'ar ta cin hanci da kuma rashawa.

Kungiyar ta nuna rashin jin dadinta da hukumar ta EFFC, tana mai cewar duk da ana tuhumar mutanen da ake zargi da cin hanci da yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa a Naijeriya, babu wani da aka daure bisa wani laifi.

Tana mai cewa aikin yaki da cin hanci da rashawa ya ja baya tun bayan da tsohon shugaban Hukumar ta EFCC Mallam Nuhu Ribadu ya bar aiki.

"Ni ban ga yadda za a yi a ce EFCC ta sha kakkausan suka da za a iya tabbatarwa ba bisa wannan rahoton," kamar yadda Femi Babafemi, mai magana da yawun EFCC ya shaida wa BBC.

'Batutuwa na zahiri da jitajita'

"An raba rahoton ne gida biyu, kashi daya an gina shi ne kan batutuwa na zahiri da gaskiya, yayin da aka gina daya bangaren kan jita-jita wadanda ba za ka iya amfani da su don cin nasara a wajen musu ba".

Yayin da aka tambaye shi cewa, akwai alamun da ke nuna yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya na ja da baya, kuma ma wasu na ganin al'amarin ya mayar da gwamnati wani fage na aikata laifukan satar dukiyar jama'a? Sai ya ce:

"A'a, idan ka duba wannan batu da ake kira cin hanci da rashawa ko almundahana, ba batu ne da ya takaita ga Najeriya ba, ruwan dare ne gama duniya.

"Amma muhimmin batu shi ne, ko akwai yunkurin yaki da matsalar, tabbas zan gaya maka akwai, kuma wannan yunkuri na ci gaba," a cewar Femi Babafemi.

Karin bayani