Shugaba Saleh na Yemen zai mika mulki

Shugaba Ali Saleh na Yemen Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Ali Saleh na Yemen

Shugaban Yemen Ali Abdullah Saleh ya rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar da za ta ba shi damar mika mulki ga mataimakinsa, abun da zai kawo karshen mulkin da ya shafe shekaru fiye da 30 yana yi.

Yarjejeniyar, wadda kasashen Larabawa na yankin Gulf suka taimaka aka kulla, ta biyo bayan watanni 9 da aka shafe ana gudanar da jerin zanga-zangar nuna adawa da shugaba Saleh.

An yi bikin sa hannu a yarjejeniyar ne a Saudiyya a gaban Sarki Abdullah da ministocin kasashen Larabawa na yankin da kuma 'yan adawar kasar ta Yemen.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon yayi magana da Shugaba Saleh ta wayar tarho, kuma ya ce,a yanzu za a dauki shi zuwa birnin New York don a ci gaba da duba lafiyarsa.

Shugaba Saleh dai ya samu rauni a wani yunkurin da aka yi na halaka shi a farkon wannan shekarar.

Karin bayani