Labaran DR Congo cikin taswira

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo kasa ce mai abubuwa da dama. Kasar na da dimbin ma'adanai da su ka hada da lu'u-lu'u da zinari, amma duk da haka al'ummar kasar na fama da matsanancin talauci.

Amfani da wannan taswira, domin ganin yadda kasar ta ke, a yayinda ta ke shirin gudanar da zabuka a karo na biyu cikin shekaru arba'in.