Shugaba Saleh yayi Allah wadai da tashin hankali a Sanaa

Shugaba Abdallah Saleh na Yemen Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Abdallah Saleh na Yemen

Rahotanni daga Yemen sun ce, an bindige mutane akalla biyar a Sanaa, babban birnin kasar, kwana daya bayan yarjajeniyar da shugabannin siyasar kasar suka sa wa hannu, jiya a Saudiya.

A karkashin yarjejeniyar dai, shugaban kasar, Ali Abdullah Saleh, ya amince yayi murabus, abinda zai kawo karshen mulkinsa na shekaru fiye da talatin.

'Yan bindiga masu biyaya ga shugaban ne suka bude wuta, a kan dubban masu zanga zangar nuna adawa da kariyar da aka ba shi daga tuhuma, a karkashin yarjajeniyar.

Shugaba Ali Abdullah Saleh zai mika ragamar mulki ga mataimakinsa ne, bayan an kwashe watanni tara ana ta zanga zangar nuna kin jininsa.

Sai dai kuma har yanzu zai ci gaba da zama Shugaban riko har nan da kwanaki casa'in.

Dubban mutane ne dai a birnin na Sanaa suka yi marhabin da labarin, to amma wasu sun yi watsi da yarjejeniyar.

Karin bayani