Shugaba Jammeh na Gambiya ya samu wa'adi na hudu

Shugaba Yahya Jammeh na Gambia
Image caption Shugaba Yahya Jammeh na Gambia

A kasar Gambiya an bayyana Shugaba Yahya Jammeh a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da akai ranar alhamis.

Yanzu shugaba Jammeh wanda ya samu kashi saba'in da biyu cikin dari na kuri'un da aka kada, ya fara wani wa'adin mulki karo na hudu a kasar.

Ya hau kujerar shugabancin kasar ne dai bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 1994.

Mutumin dake bi masa a zaben, Ousaini Darbo ya shaidawa 'yan jarida cewa zaben na cike da magudi, kuma ya yi kira ga kasashen duniya da kada su amince da sakamakon.

Dama can masu sa ido sun soki zaben --inda kungiyar ECOWAS ta kwatanta yanayin da aka gudanar da shi a matsayin mai cike da rashin gaskiya da adalci, don haka ta ki tura tawagarta ta masu sa ido.

Karin bayani