Ana Zaben 'Yan Majalisa a Morocco

Hakkin mallakar hoto Getty

Jama'ar Morocco na kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokoki.

Zaben, shine na farko tun bayan da Sarki Muhammad ya kaddamar da sauye-sauyen tsarin mulki, sakamakon guguwar neman sauyin da ta kada a kasashen Larabawa.

Sai dai rohotanni sun ce zaben bai yi armashi ba don jama'a basu fito sosai ba.

Kundin tsarin mulkin dai ya ba da karin iko ga majalisar dokoki da kuma Firayim Minista, wanda zai fito daga jam'iyyar da ke da rinjaye a majalisar.

Sai dai kuma wasu 'yan rajin kawo sauyi a Kasar sun ce sauye-sauyen ba su wadatar ba Wata mai fafutukar tabbatar da dimokuradiyya Zainab Ballami, ta fadawa BBC cewa ''Kundin tsarin mulkin, wanda daga shi ne zabukan suka samo tushe ba na dimokuradiyya ba ne, don haka ba wani sauyin da aka samu''.

Karin bayani