NATO ta kashe dakarun Pakistan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zangar adawa da kasancewar NATO a Pakistan

Rundunar sojojin Pakistan ta ce jiragen yakin kungiyar tsaro ta Nato, sun kashe dakarunta ashirin sha biyar a wani wajen binciken ababen hawa da ke arewa maso yammacin kasar, kusa da kan iyakarta da Afghanistan.

Jami'an soji sun ce an kai harin ne gab da wayewar garin ranar Asabar a yankin Mohmand mai fama da rikici.

Kakakin rundunar sojin kasashen duniya da Nato ke jagoranta a Afghanistan, ya ce suna gudanar da bincike kan lamarin.

An shafe watanni da dama Amurka na farautar masu tayar-da-kayar baya a yankunan kan iyakar Pakistan da Afghanistan.

Wannan hari dai zai dagula zaman doya da manjan da ake yi tsakanin Pakistan da Amurka.

Karin bayani