Pakistan ta datse hanyar kai kaya ga NATO

Mahukunta Pakista Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Pakistan ta fusata

Gwamnatin Pakistan ta dakatar da tura kayyayaki ga kungiyar tsaro ta NATO dake Afghanisatan bayan jirgi mai saukar ungulu na dakarun kawancen ya halaka sojojin Pakistan 25 dake kula da wani shingen binciken ababen hawa.

PMn Pakistan Raza Gilani yayi tur da harin yana mai bayyana shi da cewa ya wuce hankali. Sai dai kwamandan dakarun Nato a Afghanistan, John Allen ya bayyana alhininsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Jami'an tsaro sun shaidawa BBC cewa an basu umarni su rufe hanyar da ake tura kayan kungiyar tsaro ta NATO ta bakin iyakar kasar.

Masu tsaron bakin iyakar sun ce an maida jerin gwanon motoci a hanyoyin zuwa Afghanistan guda biyu.

Karin bayani