Baza a dage zaben Congo ba

Shugaban hukumar zaben jamhuriyar dimokradiyar Congo, ya ce za a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki a gobe, kamar yadda aka tsara.

Akwai hasashen da aka fara yi cewa mai yuwa a jinkirta zaben, saboda barkewar tashin hankali tsakanin magoya bayan 'yan siyasa dake adawa da juna, da kuma matsalar raba kayan aiki.

Jagoran 'yan adawa, Etienne Tshisekedi ya nemi shirya wani gangami na magoya bayansa a Kinshasa, babban birnin kasar, duk da wata dokar zabe dake hani ga ci gaba da yakin neman zabe.

'Yan sanda sun tsare shi har zuwa sha biyun daren jiya, lamarin da ya tilasta masa soke gangamin na karshe.