Kungiyoyi sun koka game da cin zarafin jama'a a Filato

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'in soja na sanya ido a wani waje da aka yi rikici

Kungiyoyin kare hakkin bil-Adama sun nuna damuwa dangane da cin zarafin jama'a da ake zargin jami'an tsaro na yi a karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar Filaton Najeriya, bayan tashin hankalin da aka yi a makon jiya.

Kungiyoyin sun ce hankalinsu ya tashi dangane da bayanan da suke samu na halin da mutane ke ciki a yankin inda jama'a ke zargin jami'an tsaro na kama su babu gaira-babu-dalili.

Shugabannin wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam, Comrade Sulaiman Ahmad da Gash Shamaki Peter, sun ce mutanen yankin na zargin jami'an tsaron da kashe musu 'yan uwa ba tare da sun aikata laifi ba.

Sai dai rundunar da ke aikin tabbatar da tsaro a jihar ta ce tana son tabbatar da tsaro ne, kuma ba za ta bari wasu su yi mata katsalandan ba.

A yanzu dai, an sassauta dokar hana fita baki daya da aka sa a garin daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe.

Karin bayani