An kai wani harin a jahar Yobe

Rahotanni daga Najeriya na nuna cewa mazauna garin Geidam da ke jihar Yobe sun kwana cikin yanayin zaman dar-dar bayan wani hari da wasu mutanen da ba a san ko su wane ne ba suka kai kan wani caji ofis da kuma banki a garin.

Bayanai sun ce ba'a dai samu asarar rayuka ba, amma anyi asarar dimbim dukiyoyi. Kawo yanzu mahukunta a jihar ba su yi wani cikakken bayani game da al'amrin ba.

Yanzu haka an dau tsauraran matakan tsaro a ciki garin na Geidam, inda aka girke jami'an tsaro a bakin kasuwa wajan da akai kai harin, kuma jama na korafin hana su bude shagunansu.

Karin bayani