Putin zai sake tsayawa takara a Rasha

Praministan Rasha, Vladimir Putin ya amince da zaben da jam'iyyarsa ta yi masa domin ya tsaya ma ta takarar shugaban kasa a zaben badi.

Inda ya mika godiyarsa ga irin goyan bayan da ya ce jama a kasar ta Rasha ke nuna masa.

A lokacin wani gangami na jam'iyyar URP, Mr Putin ya gargadi kasashen waje da su guji yin katsalandan a harkar zaben, yana nuna cewar wasu na biyan kudade ga kungiyoyi masu zaman kansu, domin su sauya tunanin jama'a a lokacin yakin neman zabe.

Mr Putin, wanda a baya, ya yi wa'adin mulki biyu a matsayin shugabn kasa, shi ake sa ran zai lashe zaben na watan Maris mai zuwa.

Karin bayani