Takunkumin da za a sanya wa kasar Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an kungiyar Larabawa a wajen taro kan Syria

Kungiyar kasashen Larabawa ta tsara irin takunkumin karya tattalin arzikin da take shirin sanya wa Syria, bayan gwamnatin kasar ta ki amince wa tawagar kungiyar ta shiga kasar, don ganewa idanunta irin zargin muzgunawa jama'a da ake yi wa gwamnatin.

Takunkumin ya hada da dakatar da zirga-zirgar jiragen saman Syria, ciki kuwa har da hana manyan jami'an gwamnatin kasar kai ziyara kasashen Larabawa.

Kazalika kungiyar ta dakatar da aiwatar da duk wasu harkokin kudi tsakaninta da Syria, abin da ya hada da daina hulda da babban bankin kasar.

Sannan kungiyar ta ce za a rike kadarorin Syria da ke kasashen Larabawa.

Syria ta mayar da martani

Ministan ma'aikatar waje na Syria ya soki kungiyar inda ya ce tana yin katsalandan a sha'anin kasarsa.

Ya bayyana matakan da cewa bude hanya ce don bai wa kasashen waje damar mamaye kasar.

Gidan talabijin din Syria ya ce kungiyar kasashen Larabawan na kammala aiwatar da tukunkumin karya tattalin arzikin da kasashen yamma suka sanya wa kasar ne.

Ya nuna wata zanga-zanga da magoya bayan gwamnatin kasar suka yi a sassa daban-daban na kasar, inda suke yin Alla-wadai da matakin da kungiyar kasashen Larabawan ta dauka.

Karin bayani