Syria zata fuskanci fushin kasashen Larabawa

Taron kungiyar kasashen Larabawa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Taron kungiyar kasashen Larabawa

A wani mataki da ba ta taba daukar irinsa ba, kungiyar kasashen Larabawa ta kada kuri'ar amincewa ta kakaba ma Syria takunkumin karya tattalin arziki, a kokarin tilasta ma gwamnatin dakatar da tsauraran matakan da take dauka wajen murkushe zanga zanga.

Takunkumin ya hada da hana manyan jami'an gwamnatin Syriar zirga zirga, da katse hulda da babban bankin Syria, da kuma hana saka jarin kasashen Larabawa a cikin kasar.

Ministan harkokin wajen Qatar, ya ce, za a fara aiki da matakin ne, ba tare da bata lokaci ba.

Wakilin BBC ya ce, wani abin da zai kwantar ma da Syriar hankali , shi ne cewar, makwabtanta biyu, Iraki a gabas, Lebanon a bangaren yamma, ba su goyi bayan takunkumin ba, kuma zasu iya taimakawa wajen rage ma ta radadinsa.

Karin bayani