Shugaban Yemen ya yi wa jama'a afuwa

Kwana guda bayan bada sanarwar lokacin zaben wanda zai gaje shi, shugaban Yemen , Ali Abdulah Saleh ya bada sanarwar yin afuwa ta gama -gari.

Kafafen yada labaran gwamnati sun ambaci shugaba Saleh yana cewa an yi afuwar ne ga wadanda suka tafka kura-kurai a lokacin rikicin kasar, amma banda wadanda suka yi yunkurin halaka shi.

Wata mai magana da yawun 'yan adawa, ta yi watsi da sanarwar. Ta ce a karkashin yarjejeniyar da aka cinma, kan mika ragamar iko, wadda ya sa ma hannu a makon jiya, shugaba Saleh ba shi da ikon daukar wannan mataki, tun da ya riga ya mika ikonsa ga mataimakin shugaban kasa.

Karin bayani