Dokar hana auren jinsi guda a Najeriya

Hakkin mallakar hoto 1

Majalisar dattijan Najeriya ta zartar da dokar da ta tanadi hukuncin daurin shekaru da dama ga duk wadanda suka gudanar da aure tsakanin jinsi guda.

'Yan majalisar dattijan kasar dai sun yi muhawara sosai kafin su zartar da dokar da ta tanadi daurin da ka iya kaiwa shekaru goma sha hudu ga duk wasu da suka yi auren jinsi guda.

Dokar har wa yau ta nadi hukuncin daurin da zai iya kaiwa shekaru goma ga duk wadanda suka shaida ko kuma suka taimaka aka daura auren jinsi guda.

Dama Luwadi ko Madigo haramun ne a karkashin dokokin Najeriya, kuma kungiyoyin Musulmi da Kiristocin kasar sun hada kai wajen yin Allah wadai da dabi'ar kuma suka bada gagarumin goyon baya wajen zartar da dokar.

Kafin a zartar da dokar dai, kungiyoyi da dama masu rajin kare hakkin bil'adama, sun yi ta kiraye-kirayen da kada a zartar da dokar.

Shi ma Pira Ministan Burtaniya David cameroon, ya ce duk wasu kasashen da suke samun taimako daga Burtaniya, to ya kamata su tabbatar da cewa sun hallata luwadi da madigo a kasashensu.

Batun dai ya sha suka daga shugabannin kasashen Afrika da dama da suka yi Allah wadai da kalaman nasa.

Shi ma shugaban Majlisar dattijan Najeriya David Mark a yau ya ce babu kasar da take da hakkin sanya baki a kan yadda najeriya take zartar da dokokinta.

A yanzu dai za a dakaci majalisar wakilan Najeriya ne ta zartar da doka makamancin wannan kafin a mika wa shugaban kasa ya sa hannu domin ta zama cikakkiyar doka.